Tofa: Anma Buhari Kaca Kaca

 


Bayan an kai wa wasu Bayin Allah hari a garin Zabarmari, jihar Borno, an ga bayan rayuka 43, wata kungiya mai suna CNG, ta fito ta yi magana. Gamaryyar kungiyoyin Arewa ta CNG ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi sun gaza kare rayukan al’umma. 

Da take magana game da harin, CNG ta bakin mai magana da yawunta, Abdul-Azeez Suleiman, ta ce gwamnati ba za ta iya kare ran mutanen Arewa ba. 

Vanguard ta rahoto Abdul-Azeez Suleiman ya na cewa: “Shugaban kasa da jami’an tsaro suna ta fada mana suna yin wani abu game da sha’anin tsaro.” “… amma yanzu duka mutanen Arewa sun gane cewa an yi watsi da yankinmu, an bar mu a hannun ‘yan ta’adda da suke cigaba da yi mana asara a Arewa.” A cewar Mista Abdul-Azeez Suleiman, ana yi wa yankin Arewa illa ta fuskar siyasa da tattalin arzikin kasa da wadannan mutane na ta da ake hallaka wa. 

Uzurin nan da alkawuran karya sun isa haka.” Inji CNG. 

Post a Comment

0 Comments